Lesson Notes for Hausa Language JSS1 (Basic 7) Second Term
Access free Lesson notes for Hausa Language JSS1 second term. View Basic 7 Hausa Lesson note for second Term.
SECOND TERM E- LEARNING NOTES JSS1(BASIC 7) HAUSA LANGUAGE SCHEME OF WORK
MAKO BATU
- Bita akyyukan sashen daya gabata
- Ma’anar rubutaccen adabi (maimaitawa)
- Rukunonin rubutaccen adabi
- Tsarin rubutaccen adabi
- Ma’anar sana’a
- Muhimmancin sana’a
- Ire-iren sana’o’i
- Bayanin wadansu zababbun sana’o’i
- Hanyoyin Kyautata sana’o’i
Mako na Daya(week 1) Bita akyyukan sashen daya gabata (Revision)
Mako na biyu (Week 2)
Batu (Topic) Ma’anar rubutaccen adabi:
Ma’anar rubutaccen adabi shine adabin zamani. Ana kiran wannan adabi ‘Rubutaccen adabi’ saboda da can can, tun asali, a rubuce ake tsara shi. Kuma ana kiransa ‘Adabin zamani’ Saboda bai dade sosai da shigowa ba kamar adabin gargajiya. Rubutaccen adabi ko adabin zamani ya samu ne bayan da hausawa suka iya rubutu da karatu. Hausawa kuwa, ga alama ba su iya karatu da rubutu ba sai bayan da musulinci ya shigo kasar hausa da kuma bayan turawa suka zo.
Musulinci ya shigo kasar hausa ta hannun larabawa da mutanen melle. Shi ko musulinci yana amfani da harshen larabci. Don haka da musulinci ya shigo kasar hausa, sai hausawa suka koyi rubutu da karatu irin na larabci. A hankali a hankali kuma suka kirkiro rubutun hausa da harufan larabci. Ana kiran irin wannan rubutu da sunan “Rubutun Ajami” Da rubutu ajami ne hausawa suka fara rubuta wakokin addinin musulinci da hausa.
Daga baya turawa suka shigo kasar hausa suka kafa mulkin mallaka. Su ma da suka zo sun taimaka wa hausawa wajen kirkiro rubutun boko. Shi kuma rubutun boko yana amfani da haruffan turawa. Da aka sami rubutun boko kuma sai aka shiga rubuce-rubucen littattaffan labarai, littattaffan koyon karatun boko, da wasan kwaikwayo, da sauransu.
3. Mako na uku (week 3)
Batu (Topic) Rukunonin rubutaccen adabi
Rubutaccen adabi ya rabu zuwa gida uku, kamar haka :-
- Rubutun wakoki
Wadannan su ne wakokin da aka rubuta da ajami. Wadannan wakoki da aka rubuta da boko, wadanda bayan addini, suna kuma magana a kan harkokin duniya.
b) Rubutun Zube
Wannan shi ne rubutu wanda aka yi shi ba cikin tsarin waka ba, misali kagaggun larabai wadanda ake karantawa don nishadi da kuma koyon zaman duniya da wasa kwakwalwa. Su wadannan labarai yawancisu littattafai ne wadanda ana fara yin su ne bayan da turawa suka kafa mulkin mallaka kuma hausawa sun iya karatu da rubutun boko.
c) Wasan Kwaikwayo
Wadannan wasanni ne da ake shiryawa a rubuce. Akwai kuma wasan kwaikwyon da ake shiryawa a rubuce don rediyo, akwai na talebijin , akwai kuma wanda ake yi a dandamali don yan kallo su gani.
Rabe-raben Rubutaccen Adabi
Kowane dan adam da irin baiwar da allah ya yi masa a kan kusan kowace harka ta rayuwa. A fannin adabi haka abin yake, cewa wadansu Allah ya yi masu baiwar nuna fasaharsu ga al’umma a wannan bangare ta hanyar rubutu. Ta rubutun ma akwai inda kowanne yake irin ta sa baiwar. Dangane da wannan akwai kashi uku na nau ‘o’ in rubutaccen adabi.
Na farko dai akwai wadanda su ke da baiwar iya shirya labari, Wato ta irin wadannan labarai suke nuna fasaharsu ta ba da nishadi da kumma hannunka mai sanda ga al’umma. Irin wannan nau’i na rubutaccen adabi ake yi wa lakabi da zube. Don haka Zube bangare ne na rubutaccen adabi.
Na biyu kuwa shi ne irin wadannan da ke da baiwar iya waka. Kamar zube waka ma ta hanyarta akan sami nishadi da kuma hannuka mai sanda. Ita ma dai wani bangare ne na rubutaccen adabi.
Na uku kuwa shi ne Karaminsu a duniyar Hausawa, wato rubutaccen wasan kwaikwayo. Wajen bambance shi da irin wasan kwaikwayo na asali na hausawa, sai aka yi masa lakabi da wasan kwaikwayon zamani. Don haka wasan kwaikwayo na zamani ma bangare ne na rubutaccen adabi a al’ummar hausawa
Amfanin Rubutaccen Adabi
Adabi a rubuce ko kuma azanci a rike da kowanne ciki akan sami nishadi ta karanta shi ko kuwa sauransu. Saboda haka nishadi na daga cikin irin amfanin da ake samu daga rubutaccen adabi. Bayan nishadi kuwa wani babban amfanin adabi shi ne isar da wani sako na musamman. Irin wannan sako kuwa daga tunanin mawallafin wannan adabin ne yake.
Wani babban amfanin rubutaccen adabi kuwa shi ne adana shi adabin. Wato a nan, ba kamar azancin da ke ka ba, muddin dai abu a rubuce yake, to ba za a sami ragi da kari ba. Yadda aka rubuta shi, komai dadewar zamani idan ak dauko shi, za a tarar cewa yadda aka ajiye shi haka za a same shi wato ba dadi ba ragi.
Auna fahimta:
- Menene rubutaccen adabi?
- Lissafa rukunonnin adabi guda uku (3)
Mako na Hudu:
Batu(Topic): Tsarin Rubutaccen Adabi
Rubutaccen adabi kamar yadda mukayi bayyani shi ne wanda ake kira da ‘Adabin zamani’ wannan shi ne adabin da masu ilimi suka rubuta a littafai don jama’a su karantasu kuma amfana.
Ilimin rubutu, wato yin amfani da tsara wadansu alamomi a kan takarda ko wadansu abubuwa, kamar allo, ganye dutse da makamantansu don sadar da wata magana ko sako, wacce dan Adam ya saba da fadar ta da fatar baki, a kuma saurare shi da kunne, ya samu ne ga dan Adam lokaci mai tsawo, kuma dan Adam yana yin amfani da alamomin rubutu iri-iri a sassa daban-daban na duniya. Misali mutanen kasar China (sin) suna yin amfani da wadansu alamomi masu kama da zane, ko hoto don sadar da magana a rubuce tun shekara 3,500 da suka wuce. Su kuma Jafanawa mutanen kasar Japan, suna yin amfani da wata alama guda daya tak ta wakilci gabar kalma, wato ta yi aikin baki da wasali wajen rubutu magana tun kimanin shekaru 2,000 da suka wuce.
Hausawa sun dauki irin tsarin alamomin da turawa da larabawa suke yin amfani da su. Wato alamomin nan na “abacada” suna rubutu maganarsu ta hausa da su. Watau hausawa, sun yi amfani da tsarin alamomin rubutu na Larabawa wajen maganganunsu, wannan irin tsari shi suke kira da “Rubutun Ajami”. Haka kuma, sun yi amfani da tsarin rubutun turawa na abacada, wajen rubuta maganarsu ta hausa, wannan shi suke kira da “Rubutun boko”.
Hanyoyin Nazarin Rubutaccen Adabi
A wajen nazarin rubutaccen adabi, wato zube (labari) ko wasan kwaikayo, ko waka, ana yin la’akari da wadannan muhimman abubuwa:
- Zubi da tsari
- Jigo
- Bayyanin Jigo
- Warwarar Jigo
- Salon sarrafa Harshe
A wajen nazarin rubutaccen waka, tilas ne a kulla da wadannan abubuwa guda biyar a kan kowane bangaren rubutaccen adabi Ga misali:
- Zubi da tsari: Mai yin nazarin zai yi kokari ya fito da yadda marubucin wakar ya tsara ta, wato ya kula da yadda aka fara bude wakar, ko marubucin ya fara da addu’ar budewa, ko bai fara ita ba. Mafi yawan rubutattun wakokin Hausa suna farawa ne da addu’ar budewa, inda ake neman taimako daga Allah ya dada ba da basira, da kuma yabon Annabi, kamar yadda malam sa’adu Zungur ya yi a farkon wakarsa ta Bidi’a inda ya ce:
- “Ka daura niyya a kan waka kana addu’a
A’uzu Billah daga shaidan a kan bida’a.
2.Sannan kawo basmala bisa kan rikon sunna,
Ka biya da yin hamdala ita ce wajen jama’a
3.Dafa kawo salsala don kammala da’a
Ga wanda aikensa rahama ce wajen jama’a
4 Ka iyar da kalmar salatu zuwa ga Alaye,
Da sallama ga sahabbai masu kyan dara’a
Wannan ita ce ake cew addu’ar budewa. Sai kuma a kula da yadda marubucin ya rufe ita wakar, wato ko ya rufe ta da addu’a, ko kuma da bayyana sunansa a karshe.
(ii) Jigo: Jigo Dai shi ne manufar waka, watau sakon da take dauke da shi a dunkule. A wajen nazarin waka, wajibi ne a gano jigon wakar a fito da shi a fili, a kuma fito da baiti ko a bayyana yadda mawakin ya gina jigon nasa a cikin baitocin wakar. Daga nan sai warwarar jigo, ana ne mai nazari zai yi kokari ya bayar da tasa fahimtar a kan jigon wakar, yana yin sharhi sosai tare da kowa misalai daga wakar. Idan an zo wajen nazarin waka za a ga misalai na yadda ake fito da jigo, da kuma warwarar jigo a nan gaba, cikin littafi na biyu.
- Salon sarrafa Harshe: A nan za a yi la’akari da yadda marubucin waka yayi amfani da harshe, ko yan da saukin fahimta ko ya yi wahala. Sannan kuma za a kara kula da yawan kalmomin aro na wasu harsuna kamar
Larabcida turanci da marubucin ya yi amfani da su a cikin wakar. Da irin yadda ya nuna gwanintar harshe a cikin wakar ta wajen yin amfani da karin magana, da kirari. Sai kuma a lura da yadda marubucin yayi amfani da “lugogin Harshe” wato irin dabarun jawo hankali, kamar su:
- Siffantawa
- Kamantawa/Misaltawa/kwatantawa
- Mutuntawa
- Karagiya/Luguden kalmomi
Auna Fahimta
- Wajen rubutaccen adabi, bada muhimman abubuwan da ake la’akari da su?
- Yi bayani daya daga cikin su.
Tarihin rubutun hausa
Kamar yadda ya gabata, an bayyana cewa rubutun hausa ya soma asalin ne ta hanyar amfani da alamomin rubutu na larabawa da na turawa. Yanzu sai mu dan leka mu ga dan takaitaccen tarihin wadannan hanyoyin rubutu da hausawa suka ara, suna rubuta hausa da su.
Rubutun Ajami
Wannan ita ce hanyar rubutun da hausawa suka aro daga alamomin rubutu na larabawa, inda suke yin amfani da wadannan alamomi wajen rubuta maganganun hausa.
Wannan hanyar rubutu ta samu ne a sakamakon zuwan addinin musulunci kasar hausa. Amma wani bayani ya nuna cewa tun kafin Addinin musulinci ya shigo kasar hausa, an samu wadansu larabawa yan kasuwa da suka shigo kasar hausa do yin ciniki. Su wadannan larabawa yan kasuwa sun shigo kasar hausa don harkar kasuwanci, suka hadu da hausawa suna huldar ciniki, ta wannan hanya ce, hausawa suka soma koyon alamomin rubutun larabci, suna amfani da su wajen rubuta hausa.
Rubutun Boko
Kamar Yadda addinin musulunci ya zama sanadiyar shigowar rubutun larabci, Kuma rubutun larabci yayi sanadin samuwar rubutun ajami, haka shi ma rubutun boko ya shigo cikin makwabtan hausawa na kudancin Najiriya ta fuskar addinin masihanci wato addinin Kirista. Harrufa na romawa Hausawa suka sake wa fasalin rubutu don su dace da ire-iren saututtukansu kamar dai yadda suka yi wa harrufan larabci.
Auna Fahimta
- Kafin zuwan ilmin boko ta wacce hanya ce hausawa ke rubutun adabinsu?
- Ta wani fuskar addini rubutun boko ta shigo?
Mako Biyar (week 5)
Batu(Topic) Ma’anar sana’a
Sana’a hanya ce ta amfani da hikima a sarrafa albarku da ni’imomin da dan Adam ya mallaka don bukatun yau da kullum. Don haka ke nan ana’a wata abu ce wadda mutum ya jibinci yi da nufin samun abin masarufi don gudanar da harkokin rayuwa. Sana’a abu ce wadda ta danganci tono albarkatun kasa da sarrafa hanyoyin kimiyya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da dan adam da sha’anin kasuwanci na saye da sayarwa da ciniki da sauransu. Sana’o’ in su ne mafi girma matsayi da hausawa suke amfani da su don yin dogaro da kai, su samar da abubuwan da suke bukata. Ta hanyar abin da bahaushe ya samu daga sana’arsa ne yake musanyawa ya mallaki abubuwan da ba zai iya samarwa kansa ba.
Mako na shidda (Week 6)
Batu (Topic) Muhimmancin Sana’a
- Biyan bukata
- Dogaro da kai
- Kare mutunci
- Samun abun masarufi
- Hana zaman banza
- Samar da aiki
- Koyar da sana’a
- Habaka tattalin arziki
- Kyautata hulda da juna
- Rufe asiri
- Ya sa zumunci tsakanin mai saya da mai sayarwa
- Kwautata wa al’uma
- Kasuwaci yakan sa gari ya girma(misali kano da birnin iko)
- Yakan sa chunaya tskanin kasa da kasa Misali Nijeria da China
- Samun ci gaba.
Auna Fahimta
1.Menene Sana’a
2. Lissafa muhimmancin sana’a guda biyar(5)
Aikin karshen mako
Karanta wannan takaiccen labarin sai ka amsa tambayoyin da ya biyo baya.
Muhimmancin sana’a ga ‘yan uwa mata
Daga Maimuna Yusuf Ali, No 1, Lemu rd, Tudun wada Zariya
Idan aka ce sana’a akwai sana’o’i, iri daban-daban. Mu dauki misali kamar sakar riga ta hannu na ‘fins’ ko kuma na kwarashe. In har uwargida za ta cire kunya ko in ce kyuya ta rinka yin saka, to labudda za ta samu ci gaba domin na yi na ga nasara, don ba zan manta da yadda na fara saka ba.
Don akwai wani lokaci da wata matsala ta dame ni, sai wata ‘yar uwa, kuma aminiyata ta ga halin da nake ciki, sai tana ganin mafita kawai tunda na iya saka me zai hana in rinka yi? Sai ni kuma na ce mata “Amina,” don sunanta kenan, “ba ni da inda zan rinka sayarwa.” Sai ta ce “Maimuna in dai matsalarki na gurin sayarwa ne, to ki rinka yi, in Allah ya yarda ni zan rinka dauka in kai miki makarantarmu,” don lokacin tana karatu ne, kuma tana karantarwa. Sai na ce to, don muna tafe ne a kan hanyar zuwa gidan Jagoranmu Malam Ibrahim Zakzaky.
Da na dawo gida sai na ce gaskiya maganar Amina ita ce gaskiya, kuma ga shi ba ni da kudi. Sai ta ga kwana biyu ban yi ba, sai muka kara haduwa, sai ta ce “Maimuna ya maganar saka?” Sai na ce mata gaskiya ba ni da kudi ne. Ta ce kamar nawa zai yi miki? Sai na ce ni ko nawa na samu. Sai ta ba ni har Naira dari uku. Da su na fara yin saka. Da ikon Allah ma ba ta fara dauka ba, sai mutane suka ga yadda sakar take, sai mutane suka rinka siya. Kowa ina yi musu suna saye. Da haka Allah (swt) ya rufa mani asiri ta hanyar saka lokacin da na nemi rufin asirinsa.
Sai dai kuma yanzun ba na yi kamar yadda nake yi da, saboda matsalar yara, amma ga wanda ya ga yana da lokaci, in har ‘yar uwa na son yin sana’ar ta koyi saka ko da ko huluna take yi, in ba ta iya yin saiti duka ba, da dan wannan sai ka ga ‘yar uwa na dogoro da kanta don samun ci gaba.
Abin nufi ina fata ‘yan uwa mata za su dauki wannan shawara don su amfana da ita kamar yadda na amfana da ita. To ina ganin ya kamata in sa aya sai mun sake saduwa. Don in Allah ya yarda zan ci gaba da ba ku shawara kan abin da zai taimake mu a rayuwarmu baki daya. Kuma ina mai rokon Allah ya yi mana jagoran kan abin da ya fi zama mafi alheri ga mu baki daya.
Tambayoyi
1.Wa ya rubuta wannan labari?
2. Ba muhimmancin sana’a guda(1)
3. Wace sana’a ce Maimuna ta soma a cikin wannan labari?
4. Wani matsala ta somu kafin ta soma sana’ar?
Mako na Bakwai (Week 7)
Batu (Topic )Ire-iren Sana ‘o’ in Gargajiya
Sana‘o’ in hausa na gargajiya suna da yawa, baza a iya iyakance adadinsu ba. A nan ya kamata dalibai su tuna cewa anyi masu nazarin wadannan sana’o’ in gargajiya a littafi na biyu na jerin gwanon littatafan sabuwar Hanyar Nazarin Hausa don kananan makarantun Sakandare. Domin haka a wannan darasi za a yi bitar wadannan sana ‘o’i ne ga dalibai ta hanyar rarrabe musu su dalla-dalla don samun saukin ganewa.
Idan aka dubi jimlar sana ‘o’ in gargajiya za a iya tantance su dangane da masu aiwatar da su, kamar sana ‘o’in da suka danganci maza da mata da wadanda suka yi tarayya da juna. Ga bayaninsu kamar haka.
Sana ‘o’ in Maza
Su ne wadanda yawanci maza ne suka fi yin su, ko da yake akan sami mata su yi su amma ba da yawa ba. Irin wadannan sana ‘o’ i sun hada da
- Farauta
- Gini
- Su(kamun kafi)
- Rini
- Sassaka
- Fatauci
- Tuki (mota /Jirgi)
- Noma
- Wanyanci
- Bokanci
- Dillanci
Sana ‘o’ i ne wadanda ga al’ada mata ne suke aiwatar da su daga ciki akwai
- Kitso
- Koda (casar hatsi /sussuka)
- Yin daddawa
- Kosai
- Suya cincin, alkaki
- Suya gyda ko aya
- Dafa taliyar alkama
- Yin kuli-kuli
- Yin waina
- Saka
Sana ‘o’ in Tarayya
Wannan nau’i kuma wasu sana ‘o’i ne wadanda aka yi tarraya tsakanin maza da mata wajen aiwatarwa. Al’ada ta amince wa jinsin maza da mata su gudanar da su ba wata tsangwama ba. Kadan daga cikin wadannan sana ‘o’i su ne:
- Noma
- Kasuwanci
- Dillanci
- Ginin tukwane
- Maganin gargajiya
- Kiwo
- Waka
- Lambu
Auna fahimta.
- Menene Sana’a?
- Lissafa sana’ar mata uku
- Lissafa sana’ar maza hudu
- Lissafa sana’ar tarayya uku
Masu sana’a r Gargajiya
A al’ada masu sana ‘o’ in gargajiya tamkar jini da tsoka ne tsakanin junansu, sukan hadu su taimaki junansu bisa hidimominsu na yau da gobe
Mako na takwas: (week 8)
Batu (Topic) Bayanin wadansu Zababbun sana ‘o’ i
1. NOMA
Menene Noma?
Noma na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar. Wannan shi ne kirarin sana’ar noma. Sana’ar noma ta bambanta da sauran sana ‘o’ in Hausawa. Bakamar sauran sana’o’ in ba inda kusan kowace sana’a akwai mutanen da aka sani da ita, noma sana‘ar kowani mahaluki ce. Duk wanda aka ga yana sana’ar fawa ko sana’ar kira to lalle ya gada ne daga gidansu. Amma noma sana’ar kowa ce a al’ummar hausawa. Da sarakai da malami da attajiri da talaka kowa ya gaji sana’ar noma.
A takaice dai noma tsohuwar sana’a ce wadda kowa ya duniya ya tadda ta.
Ire- iren Noma
Noma ya kasu kashi biyu. Akwai dai noma da ake yi yanayin da damina ta sauka. Damina takan yi akalla wata biyar. Wannan lokaci ne ake yin aikin damina.
Wato a yi shuka ya nuna a girbe a kawo gida. Wannan shine kashi na farko na noma, wato noman damina. Kashi na biyu kuwa shine irin noman da ake ci gaba da yi bayan daukewar ruwan sama a wurare masu dausayi da koramu. Irin wannan noma akan yi shi ta ban ruwa ne ga shukar. Wannan shi ake kira noman rani ko kuma moman rafi.
Kayan Noma Don ci
Burin kowane manomi ne da akalla ya noma abincin da zai kai shi har karshen shekara bai je ma’auna ba. Gazawa ce ga magidanci ya yi noman da bai raba shi da awo ba.
Manoma sukan noma kayan abinci kamar su gero da dawa da wake da masara da doya da rogo da dai sauransu. Bayan manomi ya ware wadataccen abinci don iyalansa wasu lokuta wasu manoma kan ware wanda za su sayar a kasuwa.
Auna fahimta.
- Menene Noma?
- Noma iri nawa ka sani? Bayyanasu
Kayan Noma Don Sayarwa.
Haka nan bayan noma kayan abinci, manomi yakan noma kayan sayarwa kamar su gyada da auduga da ridi da dai sauransu. Kudin da ya samu daga kayan sayarwa da ya noma su ke taimaka masa da sauran hidimominsa na shekara. Hidimomi na alheri da sauransu.
Bayan wannan ma manomi yakan noma kayan rafi. Wadannan kuwa su ne kamar su tumatir da albasa da kubewa da tattasai da attarugu da yakuwa da dai sauransu. Irin wadannan kayan rafi ma akan yi amfani da wasu a gida ne, wasu kuwa a sayar a kasuwa. Sannan kuma akan yi hasafi da su ga sauran yan uwa da abokan arziki.
Kayakin Aikin Manoma
Kayan aikin manoma sun hada da sungumi da magirbi da fartanya ko hauya ko kalme da garma da lauje kai wani lokaci ma har da gatari.
Wasu kayan aikin su ne manjagara ko mayayi. Akwai mandigiri ko kumbo don kaftu a fadama. Akwai magauji don yin kwarce. Akwai kuma ashasha wadda ake yin noma a tsaye da ita.
Auna Fahimta
- Lissafa kayan noma don sayar wa guda uku
- Rubuta kayan aikin manoma Guda uku(3)
2. Kiwo
Menene Kiwo?
Shi ma kamar sana’ar noma, kiwo na kowa ne. Wato ba a gadonsa. Kuma shi kiwo ba manya maza kadai aka san su da shi ba, har ma mata da yara suna sana’ar kiwo.
Akwai kiwon dabbobi kamar su awaki ko tumaki ko shanu ko raguna da dai sauransu.
Wasu sukan tanadi kiwon kaji ko agwagi ko kuma zabi.
Idan suka yi yawa akan tanadi mai aikin kiwo musamman lokacin da damina ta fadi aka yi yawa aka yi shuka. Amma idan da rani ne kowa yakan sau awakinsa da tumakinsa domin babu tsoron za su shiga gonakin mutane su yi barna. Amma kaji da agwagi babu wani abin damuwa wajen kiwonsu, domin a nan gida ko kuwa sauran gidajen na unguwar suke kiwonsu ko ma a kwararo.
Turkewa
Wannan hanya ce da mutum kan tsare dabba daya ko fiye tare da isasshen abinci don yayi musu kiwo na musamman ya sayar. Irin wannan turkewa takan kasance ko raguna ne ko kuma bunsura. Kodayake ba sai don sayarwa ba ma akan yurke irin wadannan dabbobi domin wasu bukatu kamar na layya ko kuma suna. Amma idan shanu ne yawanci akan turke bajimi ne guda daya ko kuwa guda biyu. Idan su kai yadda ake so sai kwance a je a sayar da su da kudi masu dan kauri. Wasu kam sana’arsu ke nan ta turke shanu suna sayarwa. Wasu kuma sukan turke dawaki ne. Idan sun goya su sosai sai su sai da su ga mai so. Ta irin wannan hanya ce ake kiwata dawakin sukuwa domin masu shawara irinsu. Sannan saraki ma sukan sayi goyayyun dawaki don amfani da su.
Sauran makiwata irin na sauran dabbobi da tsuntsaye ma sukan yi hakan don biyan bukatunsu na kudi idan wata bukata ta taso musu. Idan irin wannan hali na bukatar kudi ya zo sukan kama daya ko biyu gwargwadon bukatar tasu domin su sai dasu su sami kudin biyan bukatu.
Duk da haka ba a mantawa da masu kiwo na nishadi. Wato irin kiwon nan na kyanwoyi ko beran masar kai har ma da doki. Akan kiwata zomaye ko tsuntsaye kamar aku da dai sauransu.
Auna Fahimta
- Menene Kiwo?
- Bada misallan dabbobin da ake kiwo guda hudu(4)
3. Kasuwanci
Menene Kasuwanci?
A saya a sayar shine kasuwanci. Wato a nan mutum ya fitar da kudinsa ya sayi kadara, sanan wani lokaci ya fitar da wannan kadarar ya sayar shi ne kasuwanci. Mai irin wannan harka shi ne ake dan kasuwa idan mace ce kuwa akan kira yar kasuwa.
Kasuwanci ba ya yuwuwa sai da jari. Jari shi ne ake amfani da shi don sayen kadarar da za a sayar. Dan kasuwa dole ya rike jari domin ya rika jujjuya shi. Wato yakan yi amfani da jarin domin sarin kayan sayarwa Sannan idan ya sayar da kayan ya yi amfani da jarin domin sarin kayan sayarwa. Sannan idan ya sayar da su,sai ya kidaya ya gairin ribar da ya samu. Yakan gane haka bayan ya sayar da kayan, ya kidaya kudaya kudinsa, ya ware uwar kudin ya kuma ga irin abin da ya hau. Idan wani abu ya hau yakan ce an sami amfani idan kuwa uwar kudin ba ta fito ba sai ya ce, ya fadi. Saboda haka nasarar kasuwanci ita ce a ci riba. Amma idan wani dan kasuwa ya dinga faduwa a harkar saye da sayarwarsa jarinsa kullum raguwa yake har ma ya kai ga halin jarin ya bata, irin wannan hali akan ce mutum ya karye. Wato ba shi da sauran jari a hannunsa.
Dan kasuwa yakan ba da lamuni ga abokan ciniki. Haka tana faruwa ne idan ya kai kayansu wurin sayarwa kuma su masu sara su sayar ba su da wani kudi a hannunsu da za subiya nan take, sai ya lamunce musu sai su ma sun sayar sannan su kai masa nasa kudin. Wani lokaci kuma dan kasuwa yakan bada wasu kayayyaki kamar kayan haja ya lamunci abokan cinikinsa sai an fara hada-hadar kaka sannan ya zo ya karbi biyan bashinsa. Wannan hayar ma wani lokaci wasu yan kasuwar takan zame masu sanadiyar karyewa. Wani cinikin kuwa juye ban kwaryata ake yi. Hakan takan faru ne idan akwai matsnancin dukatar wannan kayan sayarwa. Wato a nan ciniki kan zama kudi hannu ne.
Ciniki yakan dauru tun daga tayi ana albarka kara dai, a’a sai ka sallama.
Akan ce to la’ada ciki ko kuwa la’ada waje? Idan la’ada ciki ne to mai sayarwa shi ke biyan la’adar idan kuwa la’ada waje ne to mai saya shi ne zai bada la’adar.
4. Dillanci
Menene Dillanci?
Dillanci sana’a ce ta karbar kayan mutum a sayar masa sa’annan shi kuma mai kayan ya biya mai sayarwar ladan dawainiyar da ya yi.
Yadda Ake Dillanci
Idan Bahaushe yana da abin da zai sayar to yakan wakilta wani mutum da yake kwararre ne ta fuskar ciniki irin wadannan kayan. Dalili kuwa wannan mutum da ake kira dillali shi ya san halin kasuwar wannan kayan. Don haka sai ya karbi kayan da ga hannun mai sayarwa ya shiga cikin gari zuwa wuraren da ya san za a bukaci wannan kaya ya kai sayar. Yawanci idan tayin ya yi wa mai kayan dadi yakan ce a karbo awalaja. Idan ko bai yi ba sai ya ce albarka. Shi mai sayen da ma yakan fara ciniki da cewa nawa aka taya? Idan an fada masa sai ya nemi ragi ko kuwa ma ya dan kara. Wani lokaci idan ya tsaya yana shawarwari sai dillalin ya ka da baki ya ce, a taya kwabo ma shi alabarka ce tasa kawai. To da zarar an sallamar da kayan akan ce la’ada ciki ko waje, sa’annan a samu a daidaita.
Su wa ke yin Dillanci?
Banamiji kadai ke sana’ar dillanci ba, Mata ma na yi. Irinsu ake kira dillaliya. Wannan kuwa yawanci kayan mata ta fi karba don sayarwa. Kuma tana bi ne gida-gida tana nuna kayan dillancinta.
Yawancin kayan dillali tufafi ne irin na maza. Dillaliya kuwa takan dau tufafi na mata. Haka kuma takan karbi kayan adon hannu ko na wuya ko na kunne ta kai talla. Takan ma dau kwanuka ko tasoshi da sauran kayan adon daki ta rika sayarwa. Shi ma dillali namiji yakan sayar da irin wadannan kaya na mata.
A halin yanzu dillanci bai tsaya kan irin wadannan kaya da aka ambata ba Dillalai sukan yi dillanci abubuwa kamar su rediyo, da agoago da gidaje kai har ma da motoci da dai sauransu.
Muhimmancin Dillalai
Babban muhimmancin dillalai shi ne sasantawa tsakanin mai abin sayarwa da kuma mai sayensa. Kuma ko da rigima ta tashi tsakanin mai saye da mai sayarwa, shi ne babban mai sheda.
Auna Fahimta:
- Menene Dillanci
- Menene muhimmancin dillanci
Mako Na Tara (week 9)
Batu (Topic) Hanyoyin Kyautata Sana’o’ in dadai da na zamani
Kamar yadda zamani ke chanzawa ababe dayawa ke dauka salo ya kuma bi zamani. Hakannan ma ta harkar sana’a Misali:
- Sana’a Noma kamar yadda muka yi bayyani noma tsohuwar sana’a ce wanda kowa ya tashi ya sa me ta. Ka fin zamani ya chanza ababen da manomi yake amfani da shi ne Fartanya, lauje, margibi da ma hudan shanu. Amma kamar yadda zamani yake chanzawa ilimi kuma na karuwa. Wannan kuwa ya kawo sauki ga sana’ar noma ta wajen amfani da trakta wajen gwara filin noma banda wannan har ma shuki wani lokaci ba sai an yi amfani da fartanya ba akan amfani da mashuki da ake hada shi da tracta a turance ana kiran sa (planter machine). Chigaba da zamani ya kawo ya kyautatawa sana’ar noma kwarai da gaskiye sabi da manomi guda yan kan noma abinci da ze ciyar da dubbin jama’a.
Zamani kuma ya taimaka da kawo iri mai yi a cikin karamin lokaci misali idan iri na masara na da yakan dauki wata biyar ya nuna na zamani kuwa zai dauki lokaci kadan misali wata biyu da rabi zuwa wata uku.
Haka ma tawajen kiwo zamani ta sa an samo wa dabbobi abinci kala- kala wadda yake sa su girma da wuri kuma su haiyafa. Bari mu dauki misali wajen kiwan kaji zamu ga cewa ana kin-kisa kwai kaza da abida ake kira a turance (incubetor machine) wannan yakan kin-kisa kwai mai yawa a dan kankani lokaci. Abincin da ake basu kuwa na zamani ne ya kan sa su girma da wuri. Ta haka kasuwancin kaji yakan bunkasa sasai.
Sana’ar saka kuwa wata sana’a ce wadda mata suke yi sukan saka hula, rigan sanyi da dai sauran. Ana anfani da kureshe wajan saka, yin saka sana’a ce wadda ke taiwaka wa mata. Zamani kuwa ta kyautata wa wannan sana’a ta wajen amfani da injin saka. Wannan yana taimaka ta wajen saka mai yawa a dan cikin lokaci.
Attakaice ce dai zamani ya taimaka wajen bunkasa sana’o’ i da yawa.
Auna fahimta.
Yi takaitaccen bayyani akan yadda zamani ta kyautawa sana.




